Jeremiah 34:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za ka tsere daga hannunsa ba amma tabbatacce za a kama ka a kuma ba da kai gare shi. Za ka ga sarkin Babilon da idanunka, zai kuwa yi magana da kai fuska da fuska. Za ka kuwa tafi Babilon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَيْ كُوَ بَذَاكَ ڟِيرَبَ، عَمَّا لَلَّيْ ذَاعَ كَامَكَ، عَبَادَكَيْ أَ حَنُّنْسَ؞ ذَاكَ غَ سَرْكِنْ بَابِيلَ عِدُواْ دَ عِدُواْ، كَكُمَيِ مَغَنَ دَشِ ڢُسْكَ دَ ڢُسْكَ؞ بَاشَكَّ ذَاكَ تَڢِے بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila.