Jeremiah 34:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
za ka mutu cikin salama. Yadda mutane suka ƙuna wutar jana’iza don girmama kakanninka, sarakunan da suka riga ka, haka za su ƙuna wuta don girmama da kuma makokinka suna cewa, “Kaito, ya maigida!” Ni kaina na yi wannan alkawari, in ji Ubangiji.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَ مُتُ ثِكِنْ سَلَمَ؞ كَمَرْ يَدَّ عَكَنْ ڧُواْنَاوَا سَرَاكُنَنْ دَ سُكَ رِغَا كَا مُتُوَ تُرَارٜىٰ، حَكَ كَيْ مَا مُتَنٜىٰ ذَاسُ ڧُواْنَ مَكَ تُرَارٜىٰ، ذَاسُيِ مَكُواْكِ دُواْمِنْكَ سُنَ ثٜىٰوَ «وَيُّواْ، سَرْكِنْمُ يَمُتُ!» نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ka mutu da salama. Kamar yadda aka ƙona wa sarakuna marigayanka turare, haka kai ma mutane za su ƙona maka turare, za su yi makoki dominka suna cewa, ‘Kaito, sarki ya rasu.’ Ni Ubangiji na faɗa.”