Jeremiah 35:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasan nan hari, sai muka ce, ‘Ku zo, dole mu tafi Urushalima don mu tsira daga Babiloniyawa da kuma sojojin Arameyawa.’ Saboda haka ne muke a Urushalima.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا لُواْكَثِنْ دَ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ نَ بَابِيلَ يَكَٰوُاْ يَاڧِ عَڧَسَرْ، سَيْ مُكَثٜىٰ وَكَنْمُ، ‹بَرِ مُشِغَ ثِكِنْ عُرُوشَلِيمَ، غَمَا مُنَ جِنْ ڟُواْرُوانْ سُواْجُواْجِنْ كَلْدِيَاوَا دَ نَ سُرِيَاوَا؞› شِيَسَا يَوْ مُنَ ظَوْنٜىٰ عَثِكِنْ عُرُوشَلِيمَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma sa'ad da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo yaƙi a ƙasar, sai muka ce, ‘Bari mu tafi Urushalima domin muna jin tsoron sojojin Kaldiyawa da Suriyawa.’ Shi ya sa muke zaune a Urushalima.”