Jeremiah 35:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَنْ‌غِنْ يُواْنَدَبْ طَنْ رٜىٰكَبْ سُنَ كِيَايٜىٰ أَبِنْدَ كَكَنْسُ يَعُمَرْثٜىٰسُ ثٜىٰوَ كَدَ سُشَا ضُوً إِنَبِے؞ غَمَا حَرْ ذُوَا يَوْ، بَسُ تَٻَ شَنْ ضُوً إِنَبِبَ، سُنَ بِيَيَّ دَ عُمَرْنِنْ كَكَنْسُ؞ عَمَّا نِے نَا يِتَيِ مُكُ مَغَنَ، كُو كُوَ بَكُيِ مِنِ بِيَيَّبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Umarnin da Yonadab ɗan Rekab ya yi wa 'ya'yansa, kada su sha ruwan inabi, sun kuwa kiyaye shi. Ba su taɓa shan ruwan inabi ba har wa yau, domin suna biyayya da umarnin kakansu. Ni kuwa na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne gare ni ba.