Jeremiah 35:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَنْ‌غِنْ رٜىٰكَبْ سُكَ أَمْسَ «بَذَامُ شَا بَ، غَمَا كَكَنْمُ يُواْنَدَبْ طَنْ رٜىٰكَبْ يَعُمَرْثٜىٰمُ، يَثٜىٰ، ‹بَذَاكُ شَا ضُوً إِنَبِے بَ، كُواْ كُو، كُواْ یَیَنْكُ حَرْ أَبَدَابَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka amsa, suka ce, “Ba za mu sha ruwan inabi ba, gama Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko 'ya'yanku, ba za ku sha ruwan inabi ba har abada,