Jeremiah 36:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Irmiya ta ɗauko wani littafi ya ba wa Baruk ɗan Neriya marubuci, kuma yayinda Irmiya yake shibtawa, Baruk ya rubuta a littafin dukan maganar da take a littafin da Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ya kuma ƙara ire-iren maganganun nan a kansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ إِرْمِيَ يَطَوْكِ وَنِ نَطَطّٜىٰنْ لِتَّڢِ، يَبَا مَرُبُوثِ بَرُكْ طَنْ نٜىٰرِيَ؞ بَرُكْ يَسَاكٜىٰ رُبُوتَ عَثِكِنْسَ دُكَنْ كَلْمُواْمِنْ دَسُكٜىٰ أَ لِتَّڢِنْ دَ سَرْكِے يٜىٰهُواْيَكِمْ نَ يَهُودَ يَڧُواْنٜىٰ أَوُتَا؞ بَنْدَ حَكَمَا، عَكَ ڧَارَ وَطَنْسُ كَلْمُواْمِ إِرِنْ وَطَنْثَنْ عَثِكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Irmiya ya ɗauko wata takarda ya ba Baruk, magatakarda, ɗan Neriya. Shi kuwa ta wurin shibtar Irmiya, ya rubuta dukan maganar da take a wancan littafi, wanda Yehoyakim Sarkin Yahuza ya ƙone a wuta. An ƙara magana da yawa kamar ta dā.