Jeremiah 36:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ka tafi gidan Ubangiji a ranar azumi ka karanta wa mutane daga littafin maganar Ubangiji da na shibta maka ka rubuta. Ka karanta su ga dukan mutanen Yahuda waɗanda suka zo daga garuruwansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، كَيْ سَيْ كَتَڢِے غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ أَ رَانَرْ أَظُمِ؞ أَوُرِنْ، سَيْ كَكَرَنْتَ عَكُنّٜىٰنْ دُكَنْ مُتَنٜىٰ كَلْمُواْمِنْ يَهْوٜىٰهْ وَطَنْدَ نَڢَطَا مَكَ كَكُمَ رُبُوتَ أَ لِتَّڢِنَّنْ؞ كَكَرَنْتَسُ عَكُنّٜىٰنْ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ وَطَنْدَ سُكَ شِغُواْ عُرُوشَلِيمَ دَغَ غَرُرُوَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
saboda haka kai za ka tafi. A ranar azumi za ka karanta wa mutane maganar Ubangiji, wadda take a takardar da ka rubuta ta wurin shibtar da na yi maka. Ka karanta ta a cikin Haikali, a gaban mutanen Yahuza waɗanda suka fito daga biranensu.