Jeremiah 37:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki Zedekiya ya yi umarni a ajiye Irmiya a sansanin matsara a kuma ba shi burodi daga titin masu gashin burodi kowace rana sai duka burodi a birnin ya ƙare. Saboda haka Irmiya ya zauna a sansanin matsara.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے صَدِڧِيَ يَبَادَ عُمَرْنِ ثٜىٰوَ عَكُلّٜىٰ إِرْمِيَ أَ ڢِيلِ نَغٜىٰڢٜىٰنْ مَاسُ غَادِ؞ عَكَ دِنْغَ بَاشِ دُنْڧُلٜىٰنْ غُرَاسَ دَغَ عُنْغُوَرْ یَنْ تُواْيَ غُرَاسَ كُواْوَثٜىٰ رَانَ، حَرْ لُواْكَثِنْ دَ عَبِنْثِ يَڧَارٜىٰ غَبَاطَيَ دَغَ بِرْنِنْ؞ حَكَ كُوَ عَكَبَرْ إِرْمِيَ عَثِكِنْ كُرْكُكُ أَ ڢِيلِ نَغٜىٰڢٜىٰنْ مَاسُ غَادِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki Zadakiya ya ba da umarni, suka sa Irmiya a gidan waƙafi. Aka riƙa ba shi malmalar abinci daga unguwar masu tuya kowace rana, har lokacin da abinci ya ƙare duka a birnin. Haka kuwa Irmiya ya zauna a gidan waƙafi.