Jeremiah 37:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarki Zedekiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya tare da firist nan Zefaniya ɗan Ma’asehiya da wannan saƙo cewa, “Ina roƙonka ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnmu saboda mu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْدَهَكَ، سَرْكِے صَدِڧِيَ يَعَيْكِ يٜىٰهُكَلْ طَنْ شٜىٰلٜىٰمِيَ دَ زَڢَنِيَ ڢِرِسْتِ طَنْ مَعَسٜىٰيَ ذُوَا وُرِنْ أَنَّبِے إِرْمِيَ دَ ثٜىٰوَ «مُنَ ضُواْڧُوانْكَ كَيِ أَدُّعَ غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْمُ أَمَدَدِنْمُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu'a ga Ubangiji Allah dominmu.”