Jeremiah 38:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Ebed-Melek ya ɗauki mutane tare da shi suka shiga ɗaki a ƙarƙashin baitulmali a cikin fada. Ya ɗauko waɗansu tsofaffin tsummoki da tsofaffi riguna daga can ya kuma zurara su da igiya wa Irmiya a cikin rijiyar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عٜىٰبٜىٰدْمٜىٰلٜىٰكْ يَطَوْكِ مُتَنٜىٰنْ يَتَڢِدَسُو غِدَنْ سَرْكِے؞ يَشِغَ طَاكِنْ أَجِيَ نَغِدَنْ سَرْكِے، يَݣُوسُواْ ڟُواْڢَڢِّنْ رِيغُنَ دَ ڟُمُّواْكِ؞ دَ إِغِيُواْيِ يَسَوْكَرْ دَسُو ذُوَا وُرِنْ إِرْمِيَ عَثِكِنْ رِجِيَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Ebed-melek ya tafi da mutanen, ya kuma tafi gidan sarki, a ɗakin ajiya, ya kwaso tsummoki da tsofaffin tufafi, ya zurara wa Irmiya a rijiyar.