Jeremiah 38:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Sarki Zedekiya ya yi wannan rantsuwa a kaɗaice ga Irmiya cewa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya ba mu numfashi, ba zan kashe ka ko in ba da kai ga waɗanda suke neman ranka ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَرْكِے صَدِڧِيَ يَرَنْڟٜىٰوَ إِرْمِيَ عَٻُواْيٜىٰ يَثٜىٰ «نَا ضَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ، اللَّهْ وَنْدَ يَكٜىٰ بَامُ رَيْ، بَذَنْ كَشٜىٰكَبَ، كُواْ إِنْمِيڧَكَ غَ حَنُّنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰسُواْ سُكَشٜىٰكَبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki Zadakiya ya rantse wa Irmiya a ɓoye, ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda yake ba mu rai, ba zan kashe ka ko in bashe ka a hannun waɗannan mutane da suke neman ranka ba.”