Jeremiah 38:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Irmiya ya ce wa Zedekiya, “Ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon, za a bar ka da rai ba za a kuma ƙone wannan birni ba; da kai da iyalinka za ku rayu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً إِرْمِيَ يَثٜىٰ وَ سَرْكِے صَدِڧِيَ «إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، اللَّهْ مَيْ ضُنْدُنَا، اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، عَتَهَنْيَ طَيَ كَطَيْ ذَاكَ رَايُ، عِتَثٜىٰ سَيْ كَمِيڧَ كَنْكَ غَ دَتَّاوَنْ سَرْكِنْ بَابِيلَ؞ إِنْ كَيِ حَكَ، بَذَاعَ ڧُواْنٜىٰ وَنَّنْ بِرْنِ دَ وُتَابَ، كَيْ دَ عِيَلِنْكَ كُمَ ذَاكُ رَايُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Irmiya ya ce wa Zadakiya, “Haka Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, idan ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila, za ka tsira, ba kuwa za a ƙone birnin da wuta ba, kai da gidanka za ku tsira.