Jeremiah 38:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba, amma duk wanda ya je wurin Babiloniyawa zai rayu. Zai tsira da ransa, ya rayu.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«إِنْجِنِ يَهْوٜىٰهْ ، دُكْ وَنْدَ يَذَوْنَ أَوَنَّنْ بِرْنِ ذَيْ مُتُ تَوُرِنْ تَكُواْبِے دَ يُنْوَ دَ بَلَعِ؞ عَمَّا دُكْ وَنْدَ يَڢِتَ يَبَادَ كَنْسَ غَ سُواْجُواْجِنْ كَلْدِيَ ذَيْ رَايُ؞ عِ، ذَيْ ڟِيرَرْ دَ رَنْسَ يَكُوَ رَايُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ubangiji ya ce wanda ya zauna a wannan birni zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma wanda ya fita ya je wurin Kaldiyawa zai rayu, zai sami ransa kamar ganimar yaƙi.