Jeremiah 38:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan fadawa kuwa suka zo wurin Irmiya suka tambaye shi, ya kuma faɗa musu dukan abin da sarki ya umarce shi ya faɗa. Saboda haka ba su ƙara ce masa kome ba, gama ba wanda ya ji zance da suka yi da sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دُكَنْ دَتَّاوَنْ سَرْكِے سُكَ تَڢِے وُرِنْ إِرْمِيَ سُكَ تَمْبَيٜىٰشِ؞ إِرْمِيَ كُوَ يَيِ مَغَنَ دَسُو بِسَغَ يَدَّ سَرْكِے يَعُمَرْثٜىٰشِ يَيِ؞ سَيْ سُكَ دَيْنَ مَغَنَ دَشِ، تُنْدَيَكٜىٰ بَا وَنْدَ يَجِ مَغَنَرْ دَ يَيِ دَسَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan sarakuna suka tafi wurin Irmiya suka tambaye shi. Shi kuwa ya amsa musu yadda sarki ya umarce shi. Sai suka daina magana da shi, tun da yake ba wanda ya ji maganar da ya yi da sarki.