Jeremiah 38:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ranka yă daɗe sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu a duk abin da suka yi wa Irmiya annabi. Sun jefa shi cikin rijiyar da ba ruwa, inda zai mutu da yunwa gama ba sauran wani burodi a birnin.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«رَنْكَيَدَطٜىٰ، يَا مَيْغِرْمَ! مُتَنٜىٰنَّنْ سُنْ عَيْكَتَ مُغُنْتَا ثِكِنْ دُكَنْ أَبِنْدَ سُكَيِ وَ أَنَّبِے إِرْمِيَ، وَنْدَ سُكَسَاشِ أَ رِجِيَ؞ ذَيْ عِيَ مُتُوَ أَوُرِنْ سَبُواْدَ يُنْوَ؞ غَمَا عَبِنْثِ يَنَدَ وُيَرْ سَامُوَ عَبِرْنِنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ya maigirma sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu da suka saka annabi Irmiya cikin fijiya, Zai mutu can da yunwa, gama ba sauran abinci a birnin.”