Jeremiah 39:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Tafi ka faɗa wa Ebed-Melek mutumin Kush, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ina gab da cika maganata a kan wannan birni ta wurin masifa, ba wadata ba. A lokacin za tă cika a idanunka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَتَڢِے يَيِ مَغَنَ دَ عٜىٰبٜىٰدْمٜىٰلٜىٰكْ مُتُمِنْ إِتِيُواْڢِيَ يَثٜىٰ مَسَ «إِنْجِنِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ، اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، غَاشِ، بَادَ جِمَاوَا بَذَنْ ثِكَ مَغَنَرْدَ نَيِ غَمٜىٰدَ عُرُوشَلِيمَ، مَغَنَرْ مَسِيڢَ بَتَأَلْحٜىٰرِبَ؞ دُكَنْ أَبُبُوَنَّنْ ذَاسُ ثِكَ أَ رَانَرْ نَنْ كُمَ ذَاكَ غَنِ دَ عِدُوانْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ka tafi ka faɗa wa Ebedmelek mutumin Habasha, cewa Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Zan sa masifa, ba alheri ba, ta auko wa wannan birni. Wannan kuwa zai faru a kan idanunka a wannan rana.