Jeremiah 39:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan dukan fadawan sarkin Babilon suka shiga suka zazzauna a Ƙofar Tsakiya. Wato, Nergal-Sharezer na Samgar-Nebo, Sarsekim wani babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da dukan sauran fadawan sarkin Babilon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً دُكَنْ دَتَّاوَنْ سَرْكِنْ بَابِيلَ سُكَ شِغَ ثِكِنْ عُرُوشَلِيمَ سُكَ ذَوْنَ عَڧُواْڢَرْ ڟَكِيَ دُواْمِنْ سُيِ مُلْكٍ بِرْنِنْ؞ عَثِكِنْسُ أَݣَويْ، نٜىٰرْغَلْ سَرٜىٰظٜىٰرْ دَ سَمْغَرْ نٜىٰبُواْ دَ سَرْسٜىٰكِمْ وَتُواْ رَبْسَرِسْ دَ وَنِ نٜىٰرْغَلْ سَرٜىٰظٜىٰرْ وَتُواْ رَبْمَكْ دَ سَوْرَنْ مَنْيَنْ دَتَّاوَنْ سَرْكِنْ بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan da aka ci Urushalima, sai dukan sarakunan Sarkin Babila suka shiga, suka zauna a Ƙofar Tsakiya. Sarakuna, su ne Nergal-sharezer, da Samgar-nebo, da Sarsekim, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan sauran shugabannin Sarkin Babila.