Jeremiah 39:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Zedekiya sarkin Yahuda da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu; suka bar birnin da dare ta hanyar lambun sarki, ta ƙofar da take tsakanin katanga biyu, suka nufi waje Araba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سَرْكِے صَدِڧِيَ نَ يَهُودَ دَ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْسَ سُكَ غَنْسُ، سُكَ غُدُ سُكَ ڢِتَ دَغَ بِرْنِنْ دَ دَرٜىٰ؞ سُكَبِے تَغُواْنَرْ سَرْكِے وَجٜىٰنْ ڧُواْڢَرْ دَتَكٜىٰ ڟَكَانِنْ كَتَنْ‌غَ بِيُ، سُكَ نُڢَ ݣُورِنْ كُواْغِنْ يُواْدَنْ أَغَبَسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Zadakiya, Sarkin Yahuza, da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu, suka fita daga birnin da dare, ta hanyar gonar sarki a ƙofar da take a tsakanin garu biyu. Suka nufi zuwa wajen Araba.