Jeremiah 40:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ni kaina zan zauna a Mizfa in zama wakilinku a gaban Babiloniyawa waɗanda za su zo wurinmu, amma ku girbe ruwan inabi, ’ya’yan itatuwa na kaka, da mai, ku zuba su a tulunan ajiyarku, ku kuma zauna a garuruwan da kuka ci.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے دَيْ ذَنْ ذَوْنَ أَ مِظْڢَ دُواْمِنْ إِنْ ذَمَ وَكِيلِنْكُ أَوُرِنْ دَتَّاوَنْ بَابِيلَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذُوَا وُرِنْمُ؞ كُو سَيْ كُيِ غِرْبِے، كُ أَجِيٜىٰ ضُوً إِنَبِے دَ یَیَنْ إِتَاثٜىٰ دَ مَنْ ظَيْتُنْ أَوُرَارٜىٰنْ أَجِيَ أَغِدَاجٜىٰنْكُ، كُذَوْنَ أَغَرُضُوً دَ كُكَثِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ni zan zauna a Mizfa, in zama wakilinku a wurin Kaldiyawa waɗanda za su zo wurinmu. Ku tattara inabi, da 'ya'yan itatuwa na kaka, da man zaitun, ku tanada su a gidajenku, ku zauna a garuruwan da kuka ci.”