Jeremiah 40:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
suka ce masa, “Ba ka san cewa Ba’alis sarkin Ammonawa ya aiki Ishmayel ɗan Netaniya ya ɗauke ranka ba?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam bai gaskata su ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَثٜىٰ مَسَ «كُواْ كَسَنِ ثٜىٰوَ سَرْكِے بَعَلِسْ نَ أَمُّوانْ يَعَيْكِ إِسْمَٰعِيلُ طَنْ نٜىٰتَنِيَ دُواْمِنْ يَذُواْ يَكَشٜىٰكَ؟» عَمَّا غٜىٰدَلِيَ طَنْ أَهِكَمْ بَيْ غَسْكَتَسُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka ce masa, “Ko ka sani Ba'alis Sarkin Ammonawa ya aiko Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe ka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam, bai gaskata su ba.