Jeremiah 41:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ishmayel ya mai da dukan sauran mutanen da suke Mizfa bayi ’ya’yan sarki mata tare da dukan sauran da aka bari a can, waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Ishmayel ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya tashi don yă haye zuwa wurin Ammonawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً إِسْمَٰعِيلُ يَݣُوشِ دُكَنْ سَوْرَنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ أَ مِظْڢَ، دُكْ دَ یَیَ مَتَ نَغِدَنْ سَرْكِے دَ سَوْرَنْ مُتَنٜىٰنْ دَ سُكَ ضَغٜىٰ؞ سُونٜىٰ نٜىٰبُظَرَدَنْ شُوغَبَنْ یَنْ غَادِنْ غِدَنْ سَرْكِے يَبَادَسُو أَ حَنُّنْ غٜىٰدَلِيَ طَنْ أَهِكَمْ يَلُورَ دَسُو؞ إِسْمَٰعِيلُ طَنْ نٜىٰتَنِيَ يَݣُوشٜىٰ مُتَنٜىٰنَّنْ، يَكَامَ حَنْيَ يَڧٜىٰتَرٜىٰ ذُوَا ڧَسَرْ أَمُّوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Isma'ilu ya kwashe dukan sauran mutanen da suke Mizfa, gimbiyoyi da dukan jama'ar da aka bari a Mizfa, waɗanda Nebuzaradan, shugaban matsara, ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Isma'ilu ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya haye da su zuwa yankin Ammonawa.