Jeremiah 41:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka bi da dukan waɗanda suka tsira daga Mizfa waɗanda ya karɓe daga Ishmayel ɗan Netaniya bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato, sojoji, mata, yara da fadawan da ya kawo daga Gibeyon
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يُواْهَنَنْ طَنْ كَرٜىٰيَ دَ دُكَنْ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِنْ دَسُكٜىٰ تَرٜىٰ دَشِ، سُكَثٜىٰثِ مُتَنٜىٰنْ دَ إِسْمَٰعِيلُ طَنْ نٜىٰتَنِيَ يَݣُوشٜىٰ دَغَ مِظْڢَ بَايَنْدَ يَكَشٜىٰ غٜىٰدَلِيَ طَنْ أَهِكَمْ؞ عَثِكِنْسُ كُوَ أَݣَويْ سُواْجُواْجِ دَ مَاتَادَ يَارَا دَ بَابَانِّ؞ دُكَنْسُ يُواْهَنَنْ يَدَاوُاْ دَسُو دَغَ غَرِنْ غِبٜىٰيُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi, suka kwashe dukan sauran jama'a, waɗanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya kamo daga Mizfa bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato sojoji da mata, da yara, da bābāni, su ne Yohenan ya komo da su daga Gibeyon.