Jeremiah 41:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai Ishmayel ɗan Netaniya da mutum goma waɗanda suke tare da shi suka kashe Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da takobi, suka kashe wannan da sarkin Babilon ya naɗa a matsayin gwamna a kan ƙasar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ إِسْمَٰعِيلُ دَ مُتَنٜىٰنْسَ نَنْ غُواْمَ سُكَتَاشِ سُكَ سَارٜىٰ غٜىٰدَلِيَ دَ تَكُواْبِے يَمُتُ؞ غٜىٰدَلِيَ شِينٜىٰ وَنْدَ سَرْكِنْ بَابِيلَ يَمَيْدَشِ ڠُومْنَنْ ڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Isma'ilu ɗan Netaniya, da mutanen nan goma da take tare da shi, suka tashi suka sare Gedaliya ɗan Ahikam ɗan shafan, da takobi, suka kashe shi, wato Gedaliya wanda Sarkin Babila ya naɗa ya zama mai mulkin ƙasar.