Jeremiah 41:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ishmayel ɗan Netaniya ya fito daga Mizfa don yă sadu da su. Sa’ad da ya sadu da su, sai ya ce, “Ku zo wurin Gedaliya ɗan Ahikam.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ إِسْمَٰعِيلُ طَنْ نٜىٰتَنِيَ يَڢِتَ دَغَ مِظْڢَ دُواْمِنْ يَسَدُدَسُو، يَنَ تَڢِيَ يَنَ كُوكَا؞ دَ يَسَامٜىٰسُ، سَيْيَثٜىٰ «كُبِے نِے ذُوَا وُرِنْ غٜىٰدَلِيَ طَنْ أَهِكَمْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Isma'ilu ɗan Netaniya ya fito daga cikin Mizfa yana kuka, don ya tarye su. Da ya sadu da su, sai ya ce musu, “Ku zo mu tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam!”