Jeremiah 41:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, rijiyar da ya zubar da gawawwakin mutanen da ya kashe tare da ta Gedaliya ita ce wadda Sarki Asa ya haƙa a matsayin kāriya saboda Ba’asha sarkin Isra’ila. Ishmayel ɗan Netaniya ya cika ta da gawawwaki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ رِجِيَرْ دَ إِسْمَٰعِيلُ يَجٜىٰڢَ جِكُنَنْ مُتَنٜىٰنْدَ يَكَشٜىٰ أَ ذَنْثٜىٰنْ غٜىٰدَلِيَ كُوَ عِتَثٜىٰ رِجِيَرْ دَ سَرْكِے أَسَ يَحَڧَ دُواْمِنْ يَڟَرٜىٰ ضُوً غَرِنْ دَغَ سَرْكِے بَعَشَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ إِسْمَٰعِيلُ طَنْ نٜىٰتَنِيَ كُوَ يَثِكَ رِجِيَرْ دَ غَوَوَّكِنْ مُتَنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Rijiyar da Isma'ilu ya zuba dukan gawawwakin mutanen da ya kashe mai zurfi ce, sarki Asa ne ya haƙa saboda tsoron Ba'asha Sarkin Isra'ila. Isma'ilu ɗan Netaniya kuwa ya cika ta da gawawwakin mutanen da ya kashe.