Jeremiah 42:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَدَ كُجِڟُواْرُوانْ سَرْكِنْ بَابِيلَ، وَنْدَ يَنْذُ شِے كُكٜىٰ جِنْ ڟُواْرُوانْسَ؞ كَدَ ڢَا كُجِڟُواْرُوانْسَ، غَمَا إِنَانَنْ تَرٜىٰ دَكُو، ذَنْ كُٻُتَرْ دَكُو دَغَ حَنُّنْسَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada ku ji tsoron Sarkin Babila, shi wanda kuke jin tsoronsa. Kada ku ji tsoronsa,’ in ji Ubangiji, ‘gama ina tare da ku, zan cece ku, in kuɓutar da ku daga hannunsa.