Jeremiah 42:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tabbatacce, duk waɗanda suka ƙudura suka tafi Masar su zauna a can za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba; ba ko ɗayansu zai tsira ko ya kuɓuta wa masifar da zan aukar a kansu.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا يَدَّ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ دَ دُكْ وَطَنْدَ سُكَ نَاثٜىٰ سُكَسَاكَيْ عَكَنْ تَڢِيَ ذُوَا مَصَرْ دُواْمِنْ سُذَوْنَ أَوُرِنْ؞ ذَاسُ مُتُ تَوُرِنْ تَكُواْبِے دَ يُنْوَ دَ بَلَعِ؞ بَابُ كُواْ مُتُمْ طَيَ وَنْدَ ذَيْڟِيرَا دَغَ مَسِيڢَرْ دَ ذَنْ كَٰوُاْ عَكَنْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk waɗanda suka sa gaba zuwa Masar domin su zauna can, da takobi, da yunwa, da annoba su ne ajalinsu. Ba wanda zai ragu, ba wanda zai tsira daga masifar da zan aukar musu.’