Jeremiah 42:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na faɗa muku yau, amma har yanzu ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku cikin dukan abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ يَوْ نَڢَطَا مُكُ، عَمَّا بَكُيِ بِيَيَّ دَ دُكْ مَغَنَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَعَيْكٜىٰنِ إِنْڢَطَا مُكُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan rana kuwa na faɗa muku abin da ya ce, amma ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku a kan kowane abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.