Jeremiah 43:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كَثٜىٰ مُسُ، ‹نِے يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا نَاثٜىٰ ذَنْ عَيْكَ بَاوَنَ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ نَ بَابِيلَ يَذُواْ نَنْ؞ ذَنْ كُمَ كَڢَ كُجٜىٰرَرْ مُلْكِنْسَ عَكَنْ دُووَڟُنَّنْ دَ إِرْمِيَ يَٻُواْيٜىٰ؞ نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ ذَيْ كُوَ كَڢَ بَبَّنْ تٜىٰنْتِنْسَ نَمُلْكِ أَوُرِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ka kuma ce musu, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ga shi, zan aika wa bawana Nebukadnezzar ya zo ya kafa kursiyin sarautarsa a kan duwatsun nan waɗanda na ɓoye. Zai buɗe babbar alfarwarsa a wurin.