Jeremiah 43:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Azariya ɗan Hoshahiya da Yohanan ɗan Kareya da dukan masu ɗaga kai suka ce wa Irmiya, “Kana ƙarya ne! Ubangiji Allahnmu bai aike ka ka ce, ‘Kada ku tafi Masar don ku zauna a can.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَظَرِيَ طَنْ هُواْشَيَ دَ يُواْهَنَنْ طَنْ كَرٜىٰيَ دَ دُكَنْ مَظَا مَاسُ طَغَ كَيْ سُكَ ڢَطَا وَ إِرْمِيَ «ڧَضْيَا كَكٜىٰيِ! يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْمُ بَيْ عَيْكُواْكَ دَ ثٜىٰوَ كَدَ مُتَڢِے، مُذَوْنَ أَ مَصَرْ بَ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai Yazaniya ɗan Hoshaiya, da Yohenan ɗan Kareya, da dukan 'yan tsagera, suka ce wa Irmiya, “Ƙarya kake yi, Ubangiji Allahnmu bai aiko ka da cewa kada mu tafi, mu zauna a Masar ba!