Jeremiah 43:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْسُ، أَݣَويْ مَظَا دَ مَاتَادَ يَارَا دَ یَنْ مَاتَانْ غِدَنْ سَرْكِے دَ دُكْ وَطَنْدَ نٜىٰبُظَرَدَنْ شُوغَبَنْ یَنْ غَادِنْ سَرْكِے يَدَنْڧَسُ أَ حَنُّنْ غٜىٰدَلِيَ طَنْ أَهِكَمْ جِيكَنْ شَڢَنْ؞ أَݣَويْ كُمَ أَنَّبِے إِرْمِيَ دَ بَرُكْ طَنْ نٜىٰرِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
mata, da maza, da yara, da gimbiyoyi, da kowane mutum da Nebuzaradan shugaban matsara ya bar wa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da annabi Irmiya, da Baruk ɗan Neriya.