Jeremiah 44:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗanda suka kuɓuta wa takobi suka komo zuwa ƙasar Yahuda daga Masar za su zama kima kawai. Sa’an nan dukan raguwar Yahuda waɗanda suka zo don su yi zama a Masar za su san maganar wane ne za tă tabbata, tawa ko tasu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
یَنْ كَطَنْ نٜىٰ دَغَ ثِكِنْسُ ذَاسُ ڟِيرَا دَغَ مُتُوَرْ تَكُواْبِے عَڧَسَرْ مَصَرْ سُكُواْمَ ڧَسَرْ يَهُودَ؞ سَعَنً دُكَنْ ضَغُواْوَرْ يَهُودَاوَا وَطَنْدَ سُكَ تَڢِے سُذَوْنَ أَ مَصَرْ ذَاسُسَنِ كُواْ مَغَنَرْ وَنٜىٰنٜىٰ ذَاتَثِكَ، كُواْ تَاوَ كُواْ تَاسُ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
‘Yan kaɗan ne za su tsere wa takobi, za su kuwa koma daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuza. Sauran mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, za su sani ko maganar wa za ta cika, tasu ko kuwa tawa.