Jeremiah 45:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَنَ نٜىٰمَنْ وَكَنْكَ مَنْيَنْ أَبُبُوَ نٜىٰ؟ كَدَ كَنٜىٰمٜىٰسُ، غَمَا يَهْوٜىٰهْ ذَيْ كَٰوُاْ مَسِيڢَ عَكَنْ دُكَنْ یَنْ أَدَمْ، عَمَّا ذَيْثٜىٰثِ رَنْكَ كَمَرْ رَبُوانْ يَاڧِ، ذَاكَ كُوَ رَايُ أَدُكْ عِنْدَ كَا تَڢِے؞ يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ يَڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kana nemar wa kanka manyan abubuwa? Kada ka neme su, gama zan kawo masifa a kan dukan 'yan adam, amma zan kuɓutar da ranka kamar ganima, a dukan wuraren da za ka tafi.’ ”