Jeremiah 46:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za su yi ta tuntuɓe; za su fāɗi akan juna. Za su ce, ‘Mu tashi, mu koma zuwa wurin mutanenmu da kuma ƙasashenmu, daga takobin masu danniya.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَسَ دَيَوَ سُنْيِ تُنْتُٻٜىٰ سُكَ ڢَاطِ؞ عِ، كُواْوَ يَڢَاطِ عَكَنْ نَكُسَدَشِ؞ سُنَ ثٜىٰوَ ‹تَاشِ، مُكُواْمَ وُرِنْ جَمَعَرْمُ، مُكُواْمَ ڧَسَرْمُ تَحَيْڢُوَ، مُغُدُ دَغَ تَكُواْبِنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْمُ!›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun yi ta fāɗuwa, Suna faɗuwa a kan juna, Sai suka ce, ‘Mu tashi mu koma wurin mutanenmu, Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gudu daga takobin azzalumi!’