Jeremiah 46:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Game da Masar. Ga saƙo game da sojojin Fir’auna Neko sarkin Masar, wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ci da yaƙi a Karkemish a Kogin Yuferites a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا سَڧُواْ غَمٜىٰدَ ڧَسَرْ مَصَرْ؞ أَ شٜىٰكَرَا تَهُطُ تَمُلْكٍ سَرْكِے يٜىٰهُواْيَكِمْ طَنْ يُواْسِيَا نَ يَهُودَ، سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ نَ بَابِيلَ يَثِ نَصَرَا عَكَنْ سَرْكِے ڢِرْعَوْنَ نٜىٰكُواْ نَ مَصَرْ دَ سُواْجُواْجِنْسَ؞ وَنَّنْ يَڢَرُ نٜىٰ أَ كَرْكٜىٰمِشْ كُسَدَ كُواْغِنْ يُڢِرٜىٰتِسْ؞ غَا مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ غَمٜىٰدَ سُواْجُواْجِنْ مَصَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.