Jeremiah 46:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sojojin da ta yi hayarsu a cikinta suna kamar ’yan maruƙa masu kitse. Su ma za su juya su kuma gudu gaba ɗaya, ba za su iya tsayawa ba, gama ranar masifa tana zuwa a kansu, lokacin da za su sha hukunci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُواْجُواْجِنْ هَيَرْ دَسُكٜىٰ عَثِكِنْتَ كَمَرْ یَیَنْ شَانُو نٜىٰ مَاسُيَوَنْ ڧِبَ؞ سُو مَا سُنْجُويَا سُنْ‌غُدُ، بَسُ عِيَ ڟَيَاوَا سُيِ يَاڧِبَ؞ غَمَا رَانَرْ مَسِيڢَرْسُ تَ إِسُواْ، لُواْكَثِنْ حُكُنْثِنْسُ كُمَ تَذُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙa ne, masu yawan kitse, Sun ba da baya, sun gudu, ba su tsaya ba, Domin ranar masifarsu ta zo, Lokacin halakarsu ya yi.