Jeremiah 46:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Masar za tă yi huci kamar macijin da yake gudu yayinda abokin gāba yana matsowa da ƙarfi; za su fāɗo mata gatura kamar mutanen da suke saran itatuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُواْڟِنْ غُدُنْ مَصَرْ كَمَرْ مُواْڟِنْ غُدُنْ مَثِيجِنٜىٰ، غَمَا أَبُواْكَنْ غَابَنْتَ سُنَ ذُوَا دَ ڧَرْڢِے، سُنَ ذُوَا مَتَ دَ غَاتَرِ كَمَرْ مَاسُ سَارَنْ إِتَاثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Masar tana gudu, tana huci kamar maciji, Gama abokan gābanta suna zuwa da ƙarfi, Za su faɗo mata da gatura kamar masu saran itatuwa.