Jeremiah 46:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila. Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nisa, zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yaƙub zai sāke kasance cikin salama, rai kwance, babu kuma wanda zai sa ya ji tsoro.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«يَنْذُ ڢَا، يَا كُو ذُرِيَرْ بَاوَنَ يَعْڧُوبَ، كَدَ كُجِڟُواْرُواْ، يَا كُو ذُرِيَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كَدَ كُڢِرْغِتَ! غَاشِ، ذَنْثٜىٰثٜىٰكُ دَغَ ڧَسَا مَيْ نِيسَ، ذَنْثٜىٰثِ یَیَنْكُ دَغَ ڧَسَرْ بَوْتَا؞ ذُرِيَرْ يَعْڧُوبَ ذَاسُ دَاوُاْ، ذَاسُ كَسَنْثٜىٰ دَ لَاڢِيَ دَ سَلَمَ، بَابُوَنْدَ ذَيْسَاكٜىٰ ڟُواْرَتَرْ دَسُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ya bawana Yakubu, kada ka ji tsoro, Kada ka firgita, ya Isra'ila. Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa da rai kwance, Ba wanda zai razanar da shi.