Jeremiah 48:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا كٜىٰ غَرِنْ سِبْمَ، ذَنْيِ كُوكَا دُواْمِنْكِ ڢِيٜىٰدَ يَدَّ نَيِ دُواْمِنْ غَرِنْ يَظٜىٰرْ نَ أَمُّوانْ؞ يَا كٜىٰ سِبْمَ، كِنَ كَمَ دَ إِتَاثٜىٰنْ إِنَبِے وَنْدَ رَسَّنْكِ سُنْ بَظُو حَرْ تٜىٰكُنْ يَظٜىٰرْ؞ عَمَّا يَنْذُ مَيْ هَلَّكَرْوَ يَڢَاطُواْ عَكَنْ غِرْبِے، عَكَنْ یَیَنْ إِتَاثٜىٰنْ ٻَوْرٜىٰنْكِ دَ یَیَنْ إِنَبِنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan yi kuka saboda kurangar inabin Sibma Fiye da yadda zan yi kuka saboda mutanen Yazar. Rassanku sun haye teku har sun kai Yazar, Amma mai hallakarwa ya faɗo a kan 'ya'yan itatuwanku da damuna Da kan amfanin inabinku.