Jeremiah 49:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi kirarin yaƙi a kan Rabba ta Ammonawa; zai zama tarin juji, za a sa wuta a ƙauyukan da suke kewayenta. Sa’an nan Isra’ila zai kori waɗanda suka kore shi,” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَڧِيڧَ، ݣُونَكِے سُنَ ذُوَا دَ ذَنْسَا رَبَّهْ، بَبَّنْ بِرْنِنْ أَمُّوانْ، تَجِ بُوسَرْ ڧَهُوانْ يَاڧِ؞ رَبَّهْ ذَاتَ ذَمَ كُڢَيْ، ذَاعَ ڧُواْنٜىٰ ڧَوْيُكَنْتَ دَ وُتَا؞ سَعَنً إِسْرَٰٓءِيلَاوَا ذَاسُ مَلَّكِ وُرَارٜىٰنْ دَ أَمُّواْنَاوَا سُكَ ڨُوثٜىٰ سُكَ مَلَّكٜىٰسُ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka lokaci yana zuwa, Sa'ad da zan sa mutanen garin Rabba ta Ammon su ji busar yaƙi. Rabba za ta zama kufai, Za a ƙone ƙauyukanta da wuta, Sa'an nan Isra'ila zai mallaki waɗanda suka mallake shi. Ni Ubangiji na faɗa.