Jeremiah 49:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Damaskus ta karai ta juya don ta gudu tsoro kuma ya kama ta; wahala da zafi sun kama ta, zafi kamar na mace mai naƙuda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دِمَشْڧُ تَذَمَ مَرَرْ ڧَرْڢِے، تَجُويَا دُواْمِنْ تَغُدُ؞ ڟُواْرُواْ يَكَامَتَ، عَذَابَ دَ بَڧِنْ ثِكِ سُنْ كَمَاتَ، كَمَرْ مَثٜىٰنْ دَتَكٜىٰ ثِكِنْ ذَاڢِنْ نَڧُدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dimashƙu ta yi halin ƙaƙa naka yi, Ta juya, ta gudu, Tsoro ya kama ta, Azaba da baƙin ciki sun kama ta kamar na naƙuda.