Jeremiah 49:28 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Game da Kedar da mulkokin Hazor, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fāɗa wa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tashi, ku fāɗa wa Kedar ku kuma hallaka mutanen Gabas.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا سَڧُوانْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا غَمٜىٰدَ مُتَنٜىٰنْ كٜىٰدَرْ دَ سَرَاكُنَنْ يَنْكِنْ حَزُوارْ، وَطَنْدَ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ نَ بَابِيلَ يَثِ دَ يَاڧِ؞ إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، «كُو سُواْجُواْجِنْ بَابِيلَ، تَاشِ، كُتَڢِے كٜىٰدَرْ، كُهَلَّكَ مُتَنٜىٰنْ يَنْكِنْ غَبَسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Kedar da sarakunan Hazor, waɗanda sarki Nebukadnezzar ya ci da yaƙi, “Ku tashi zuwa Kedar, Ku hallaka mutanen gabas.