Jeremiah 49:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ku yi maza ku gudu! Ku zauna a kogo masu zurfi, ku da kuke zama a Hazor,” in ji Ubangiji. “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya shirya muku maƙarƙashiya; ya ƙulla maƙarƙashiya a kanku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُو مَذَوْنَنْ حَزُوارْ، كُغُدُ ذُوَا نٜىٰسَ، كُٻُيَ! نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞ غَمَا سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ نَ بَابِيلَ يَغَمَ شِرِنْسَ عَكَنْكُ، شِرِنْ يِنْ غَابَادَكُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ku mazaunan Hazor, ku gudu zuwa nesa, Ku ɓuya cikin zurfafa, ni Ubangiji na faɗa, Gama Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya shirya muku maƙarƙashiya, Ya ƙulla mugun nufi game da ku.