Jeremiah 5:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku, za su cinye ’ya’yanku maza da mata; za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku, za su cinye ’ya’yan inabinku da na ɓaurenku. Da takobi za su hallaka biranenku masu katanga.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاسُثِنْيٜىٰ أَمْڢَانِنْ غُواْنَرْكُ دَ عَبِنْثِنْكُ؞ ذَاسُ هَلَّكَ یَیَنْكُ مَظَا دَ مَاتَا، ذَاسُثِنْيٜىٰ غَرْكُنَنْكُ نَتُمَكِ دَ نَشَانُو؞ ذَاسُثِنْيٜىٰ غُواْنَكِنْ إِنَبِنْكُ دَ عِتَتُوَنْ ٻَوْرٜىٰنْكُ؞ دَ كَايَنْ يَاڧِنْسُ ذَاسُ هَلَّكَ بِرَنٜىٰنْكُ مَاسُ كَتَنْ‌غَ وَطَنْدَ كُكٜىٰ دُواْغَضَ عَكَيْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku. Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza. Za su cinye garkunanku na tumaki, da na awaki, da na shanu, Za su kuma cinye 'ya'yan inabinku da na ɓaurenku. Za su hallaka biranenku masu kagara da takobi, waɗanda kuke fariya da su.