Jeremiah 50:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda fushin Ubangiji ba za tă zauna a cikinta ba amma za tă zama kufai gaba ɗaya. Duk waɗanda suka wuce Babilon za su ji tsoro su kuma yi tsaki saboda dukan mikinta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ ڢُشِنْ يَهْوٜىٰهْ ، بَابِيلَ ذَاتَ ذَمَ وُرِنْ دَ بَاوَنْدَ ذَيْ ذَوْنَ عَثِكِ، ذَاتَذَمَ كُڢَيْ سُواْسَيْ؞ دُكْ وَنْدَ يَبِے تَوَجٜىٰنْ بَابِيلَ، ذَيْ رَسَ أَبِنْ ڢَطَا، ذَيْ كُمَجَا ڟَكِ سَبُواْدَ مَسِيڢَرْ دَ تَسَامٜىٰتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda fushin Ubangiji, ba wanda zai zauna a cikinta, Za ta zama kufai, Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zai ji tsoro, Zai kuma yi tsaki saboda lalacewarta.