Jeremiah 50:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da waɗanda suke zama a Fekod. Ku fafara, ku kashe kuma hallaka su sarai,” in ji Ubangiji. “Ku aikata dukan abin da na umarce ku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، «أَ هَوْرَ ڧَسَرْ مٜىٰرَتَيِمْ، أَ ڢَاطَ مَتَ دَ يَاڧِ، أَ ڢَاطَوَ مَذَوْنَنْ ڢٜىٰكُوادْ دَ يَاڧِ؞ عَبِيسُ، عَكَشٜىٰسُ، أَ هَلَّكَرْ دَسُو كَكَڢْ؞ عَيِ دُكَنْ أَبِنْدَ نَعُمَرْتَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ku haura ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da mazaunan Fekod. Ku kashe, ku hallaka su sarai, Ku aikata dukan abin da na umarce ku, Ni Ubangiji na faɗa.