Jeremiah 50:33 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “An danne mutanen Isra’ila, haka ma mutanen Yahuda. Dukan waɗanda suka kama su suna riƙe su kankan, suna kin barinsu su tafi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ، «أَنْيِ وَمُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَنِّيَ، أَنْكُمَيِ وَمُتَنٜىٰنْ يَهُودَ دَنِّيَ؞ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكَ كَامَسُ، سُنْ رِڧٜىٰسُ بَايِ دَ ڧَرْڢِے، بَسُ يَرْدَ مُسُ سُتَڢِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, An danne mutanen Isra'ila da na Yahuza, Duk waɗanda suka kama su bayi sun riƙe su da ƙarfi. Sun ƙi su sake su.