Jeremiah 50:44 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai dausayi, zan fafare Babilon daga ƙasan nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa domin wannan? Wane ne kamar ni da zai kalubalance ni? Kuma wanda makiyayi zai iya tsaya gāba da ni?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَمَرْ يَدَّ ذَاكِ يَكَنْ ٻُلُّواْ دَغَ ثِكِنْ كُرْمِ نَبَاكِنْ كُواْغِنْ يُواْدَنْ يَكُمَ كُواْرِ غَرْكٜىٰنْ تُمَكِ دَغَ ڢِيلِنْ كِيوُاْ، حَكَ ذَنْ ٻُلُّواْ إِنْ كُواْرِ بَابِيلَ ڢَرَتْ طَيَ دَغَ ڧَسَرْتَ؞ شُوغَبَنْدَ ذَنْ ذَاٻَا، شِے ذَيْ يِمُلْكِنْتَ؞ غَمَا وَنٜىٰنٜىٰ كَمَرْنِ؟ وَ كُمَ ذَيْ عِيَيِنْ ڧَارَتَ؟ إِنَا مَكِيَايِنْ دَ ذَيْ عِيَ ڟَيَاوَا يَيِ غَابَادَنِے؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ni Ubangiji ina zuwa kamar zakin da yake fitowa daga kurmin Urdun zuwa makiyaya. Nan da nan zan sa su gudu daga gare ta. Sa'an nan zan naɗa mata wanda na zaɓa. Wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Wane shugaba zai yi gāba da ni?