Jeremiah 50:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama zan kuta in kuma kawo a kan Babilon haɗinkan manyan al’ummai na arewa. Za su ja dāgār gāba da ita, kuma daga arewa za a ci ta da yaƙi. Kibiyoyinsu za su zama kamar na gwanayen jarumawa waɗanda ba sa dawowa hannu wofi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، ذَنْتَادَ تَارُوانْ مَنْيَنْ أَلْعُمَّيْ، دَغَ أَرٜىٰوَ ذَاسُذُواْ سُڢَاطَوَ بَابِيلَ؞ ذَاسُ جٜىٰرَ كَنْسُ دُواْمِنْ ڢَارَ يَاڧِ غَابَادَ عِتَ، ذَاسُ كُوَ ثِنْيٜىٰتَ؞ كِبِيُواْيِنْسُ كَمَرْ نَمَاسُ عِيَ يَاڧِ نٜىٰ، وَطَنْدَ بَسُ كُواْمُواْوَ حَنُّ وُاْڢِ دَغَ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shi, zan kuta manyan ƙasashe daga arewa Su faɗa wa Babila da yaƙi. Za su ja dāgar yaƙi gāba da ita, su cinye ta. Kibansu kamar na gwanayen mayaƙa ne Waɗanda ba su komowa banza.