Jeremiah 51:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da zatinsa, ya ce Tabbatacce zan cika ka da mutane kamar fāra, za su kuwa yi sowa don nasara a kanka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا يَرَنْڟٜىٰ دَ كَنْسَ يَثٜىٰ، ذَيْثِكَ بَابِيلَ دَ سُواْجُواْجِنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْتَ، ذَاسُيِيَوَ كَمَرْ ڧُنْغِيَرْ ڢَارِ، ذَاسُ تَادَ مُرْيَرْ نَصَرَا عَكَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Mai Runduna ya rantse da zatinsa, ya ce, “Hakika zan cika Babila da mutane kamar fāra, Za su kuwa raira waƙar nasara a kanta.”